Matatun Man Najeriya na tace lita Miliyan 6.76 a kowace rana. Wannan ya fito ne daga bakin Ohi Alegbe, Babban Daraktan labarai na NNPC inda yake bayyana haka a Abuja.
Matatan Mai
Matatun Mai sun kara daga Man da suke tacewa bayan da aka daga darajar su kuma suka dawi aiki makonnin sa suka wuce.
Matatar Mai ta Fatakwal na tace Mai lita Miliyan 4.09 a kowacce rana. Ita kuma ta Kaduna tana tace Miliyan 1.29 a kowacce rana. Sanna ta Warri tana tace Miliyan 1.38 a kowacce rana.
Ana sa ran zuwa karshen watan Janairu zasu iya tace Lita Miliyan 10 a kowacce rana.
The post Matatun Man Najeriya Na Tace Lita Miliyan 6 Kullum appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on YESNAIJA.COM.