Shugaban hukumar EFCC ya bayyana cewa hukumar zata kama wasu manyan mutane a najeriya nan bada dadewa ba.
Ibrahim Magu, shugaban hukumar EFCC
Ibrahim Magu wanda shine shugaban hukumar, ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da yan jarida a jiya. Ya bayyana cewa: “Akwai wasu manya wadanda munanan muna bincikar su, zuwa sati mai zuwa zasu gurfana a gaban kotu. Ina tabbatar maku EFCC ba zata kyale wani babban mutum ba.”
Sannan kuma Magu ya bayyana cewa tsoron Allah da kishin kasa kasa ya sanya shi yake yin aiki ba sani ba sabo. Kuma ya bayyana cewa giyon bayan da shugaba Buhari yake basu yana taimaka masu matuka.
Ya bayyana cewa hakayar shugaba Buhari na kikatin yaki da rashawa na taimaka masu matukar gaske.
The post Zamu Kama Wasu Manyan Mutane – Shugaban EFCC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.