Manyan Labarai Guda 11 Wadanda Sukayi Fice A Ranar Talata


YESNAIJA.COM ta tattara maku manyan labarai guda 11 wadanda sukayi fice a ranar Talata 6 ga watan Janairu 2026. Ku duba domin ku same su.

olisa metuh

Olisa Metuh, jami’i mai hudda da jama’a na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP)

1. EFCC Taje Gidan Metuh, Ta Kama Shi
EFCC ta kama jami’i mai hudda da jama’a na PDP inda take zargin shi ta cin haramtattun kudaden tsaro.

2. Tsohon Ciyaman Din PDP Ya Gurfana Gaban Kotu
Tsohon ciyaman din PDP Halliru Bello ya gurfana a gaban kotun Abuja.

3. Matar Nnamdi Kanu Ta Haihu
Matar Nnamdi Kanu, Daraktan Rediyon Biafra ta hauhu.

4. A Saki Kanu Ko Mu Tada Rikici – Tsagerun Naija Delta
Wata kungiyar tayi barazanar cewa idan ba a saki Nnamdi Kanu ba zata tada rigima. Kungiyar NDPDF ce tayi wannan barazanar.

5. AIT Sun Kaima Buhari Kyau
Gidan Talabijin na AIT ya kaima shugaban kasa katin taya shi murnar Maulidi da kuma Kirisimeti.

6. Abunda Buhari Ya Fada Ma Shugabar IMF
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana ma shugabar IMF cewa Najeriya zata duba inda kudaden ta ke makalewa domin hana almundahana da kuma tabbatar da karuwar kudaden shiga.

7. EFCC Na Bincikar Femi Fani-Kayode                                                                                                                                                                     Jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewa EFCC ta samu wani koke akan Femi Fani Kayide, kuma tana  cikin bincikar shi a halin yanzu.

8. Yan Shi’a Sun Bayyana Sunan Wanda Ya Mutu A Hannun Sojoji
Yan Shi’a sun bayyana cewa Abbas Isiyaku shine wanda ya mutu a hannun sojoji yayin da suke rike dashi.

9. Matarun Man Najeriya Na Aiki Sosai
Matatun Mai na Kaduna, Fatakwal da Warri na tace Mai Kimanin lita Miliyan 6.76 a kowace rana.

10. PDP Ta Maganta Akan Tsare Metuh
Jam’iyyar PDP ta maganta akan tsare Olisa Metuh da EFCC tayi. Ta bayyana cewa hukumar na shirin kashe shi ne.

11. Dan Yakubu Gowon Ya Fito Daga Kurkukun Amurka
Dan tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya fita daga kurkuku bayan ya share Shekaru 22. A ranar 1 ga watan Janairu aka sake shi.

The post Manyan Labarai Guda 11 Wadanda Sukayi Fice A Ranar Talata appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on YESNAIJA.COM.