Za’a Gudanar Da Zabuka A Biafra – Uwazurike


Shugaban kungiya mai neman fafitikar kafa kasar Biafra (MASSOB), Ralph Uwazurike bayyana cewa zata bada umurni a gudanar da zabuka a Biafra.

biafra nwazurike

Ralph Uwazurike, shugaban kungiyar MASSOB

Zabukan zasu kasance na Kansila, Dan majalisa da Gwamnoni. Shugaban kungitar Uwazurike ne ya bayyana haka.

Ya bayyana cewa Fada Samuel Aneibdom ne zaya zama shugaban hukumar zaben. Kuma ya bayyana cewa zaben za’ayi shi ba kamar irin na Najeriya ba wanda ake magudi.

Uwazurike ya bayyana cewa daga 22 ga watan Febrairu za’a gudanar da zaben. Ya bayyana cewa su suna kokarin kafa Biafra ne bata hanyar rikici ko tashin hankali ba

The post Za’a Gudanar Da Zabuka A Biafra – Uwazurike appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.